Bukatar Karrama Likitar Da Ta Taimaka Wajan Tsaida Yaduwar Ebola a Najeriya

An shiga kiraye-kirayen a karrama Likitar nan da ta kare ‘yan Najeriya da dama daga kasadar kamuwa da cutar Ebola, wato marigayiya Dr. Ameyo Adedavoh.An dan kwan biyu da hukumomin duniya su ka tabbatar da baratar Najeriya daga mugunyar cutar nan ta Ebola, kuma har an ma fara mancewa da cutar a Najeriya.

To amma wasu kungiyoyi da fitattun ‘yan Najeriya na cewa bai kamata a mance da Dr. Adadevoh ba, wadda ta hana dan Laberiya marigayi Dr. Patrick Sawyer baza cutar, ta wajen killace shi a asibiti da ya iso Najeriya; amma ta yi ta jinyarsa har ita ma daga baya cutar ta yi ajalinta.

Prof. Balarabe Sani Garko Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria yace

Ita ma Dr. Amina Lami Abdullahi da ke Kwalejin Kimiyya Da Fasaha ta Kaduna, ta ce

Idan ba a mance ba dai, marigayiya Dr. Ameyo Adadevoh, wadda ta yi karatu a Ingila, nan da nan ta killace mutumin da ya fara kawo Ebola daga Laberiya zuwa Najeriya, wato Dr. Patrick Sawyer a asibiti, duk kuwa da matsin lambar wasu manya wai ta sake shi, ciki har da Jakadan Liberiya a Najeriya, amma ta ki saboda kar ‘yan Najeriya su kamu. To saidai ta yi ta masa jinya; karshenta ma, garin jinyarsa ta kamu da cutar ta mutu.

Shugabar kungiyar kare muradun matasa a Najeriya ta Youth Alive Foundation, Udy Okon, ta ce jinkirta zabe a Najeriya na bai wa ‘yan Boko Haram kwarin giwar cewa, yawan amfani da ‘yan mata wajen kai hari na da wata fa’ida garesu kamar firgita hukumomi da sauran jama’a, don haka bai kamata a rika dage zabe ba da sunan tsaro in ji ta.