Cigaban Da Na’ura Mai Kwakwalwa Ta Kawowa Mallam Bahaushe

Na’ura mai kwakwalwa dai ta kawo cigaba a duniyar mallam bahaushe, idan aka duba a baya shekaru da suka wuce za’a ga cewar mutane da dama suna jin sunan kamfuta ne da aikin da take kawai, kasancewar rashin wadatar ta a wannan lokacin, amma yanzu idan aka duba kasar mallam bahaushe birni da kauye baza’a rasa wannan na’ura mai kwakwalwa ako ina ba.

Dangane da abin da ya shafi komfuta, za’a ga cewa cigaban data kawo a cikin al’ummar hausawa to abin sai godiya. Kafin duniyar kwamfuta dai mutane dayawa na daukar wannan na’ura a matsayin wani abune da ba yadda za’a yi kowa ya iya sarrafa ta, biyo bayan illimin fasahar komfuta a wannan zamani, mutane dayawa sunyi la’akarin cewa wata abace da mutum ke bukata wajen gudanar da rayuwa.

Ganin irin cigaban da ita wannan na’ura ta kawo ga al’ummar hausawa, hakan ya jawo hankulan mutane dayawa wajen amfani da ita kamar wajen koyar karatu na boko da Arabiya, kuma ba karamin taimako bace ga malamai da ‘dalibai a makarantu.

Na’urar kamfuta ba karamin taimako bace ga mallam bahaushe, idan aka duba yadda ta kulla alaka tsakanin mutane da sanin abubuwan dake wakana a duniya, kasancewar ba sai mutane sun saurari labarai daga gidajen radiyo da talabishin kafin sanin me duniya ke ciki.