Dandalin YouTube na murnar cika shekaru goma da kafuwa akan yanar gizo, hakan na nufin shekaru goma kenan tunda Jawed Karim ‘daya daga cikin matasan da suka kirkiro dandalin ya kafe hotan bidiyo na farko kan dandalin.
Shekara ‘daya da kirkiro dandalin YouTube, matasan su uku Jawed Karim, da Chad Hurley da Steve Chen, suka sayar da Dandali ga kamfanin fasaha na Google akan kudi dalar Amurka biliyan ‘daya da miliyan sittin da biyar.
Bayan da Youtube ta koma mallakar Google, ta kuma cigaba da habaka da janyo hankalin mutane. Wani nazari yace dandalin youtube shine shafin yanar gizo na uku acikin shafukan da mutane suka fi ziyara kan yanar gizo, biyo bayan shafin Google dana Facebook. Wanda a yanzu haka yake da mutane miliyan 800 da suke amfani da shi, kuma mutane na zuba sabbin hotannan bidiyo sama da 300 a cikin dakikoki sittin.
Abaya lokacin da aka kirkiri wannan dandali a shekara ta 2005, a kwai hanyoyin da ake wajen zuba bidiyo kan shafin masu wahala, amma youtube ta canza duk hanyoyin ta mai da su masu sauki.