‘Dan Iya Ya Gano Hanyar Sauke Masu Mukamin Siyasa

Wasu magoya bayan kakakin majalisar wakilai Aminu Waziri Tambuwal, suka kutsa da shi cikin majalisa duk da yunkurin ‘yan majalisa na hana shi shiga.

A karkashin wata bishiya na hangi ‘Dan Iya yau yana wani fadi, nace ah lallai ‘Dan Iya yau ana cikin nishadi, kodai kayi katarin kicibus da wani dan siyasa ne ya baka kudi?

‘Dan Iya yace, kai dai bari kawai na Ikira ina cikin wani rudi saboda na lakanci al’umar kasar mu basa jin dadi, kaga garjejen saurayi yana tafiya kan hanya yana ta tangadi, idan anyi korafi ‘yan siyasa su rinka wani kaudi saboda sun san zabon kasar mu ya koma nadi, shiyasa da an gama zabe suka shiga ofis kai da ganin su kuma sai badi, wannan ne yasa rayuwar talakan kasar nan ta tabarbare saboda babu wani budi.

Nace Eh to amma ‘Dan Iya kada ku bari ‘yan siyasa su mayar daku wasu bebaye, saboda sun saba neman yakin zabe na yane yane, sun maida matasan kasar mu da ya kamata a mora ‘yan shaye shaye, kullun suka fita yakin neman zabe sai su rinka narka musu kayan maye, amma da sunzo dandamalin dire jawabi sai kaji suna zamu kawo sauye sauye, sai dai da zarar sunci zaben sai su mayar damu wawaye, amma fa yana da kyau ‘Dan Iya kasan ‘yan ‘kasa suna iya jirwaye don kuwa dokar kasar mu ta tanadi kiraye, idan aka zabi wakili ya buge da nanaye zamu iya dawo dashi gida don tura gwanaye.

‘Dan Iya yace, yawwa yanzu kam sai nace nagode Allah, domin kuwa yanzu babu ruwana da wata wala wala, idan naga ‘dan siyasa na kokarin maidani wani gaula kokuma ya fara mana wala wala, sai mu lallabashi ya sai ya shiga daula mu hada kanmu guri guda domin daukar mataki, saboda acikin dokar kasar mu akwai wata sala, wadda tabamu mu warware duk ‘daurin da aka kulla har sai mun tabbatar da wakilan da suka buge da tsilla tsalla sun dawo cikin mu Alabarshi a sake sabon lala, kaga daga nan bamu ba wahalar maula.

Nace, to ‘Dan Iya Allah yasa muma mu rike gaskiya, kada mu bari wani ‘dan siyasa ya bamu toshiya ko kuma yayi rufdugun rufe mu da ‘karya a karshe ya hadamu da hayaniya, ko ya buge barin mu cikin wuya, abinda yakamata shine mu dauki rigar juriya mu kuma dunga rika nunar da junan mu bukatar zaman lafiya, saboda koda ace anyi mana chogen zabe ko kwa murdiya, to ai a kwai ranar ramuwar da zamu gauraya ranar da zamuyi kiranyen wadanda suka gajiya su dawo baya.