Wani mazaunin jihar Ohio, daya tsayar da wani ‘dan sandan ciki, a lokacinda yayi shigan burtu, ya nuna cewa shi jami’in ‘yan sanda ne, an yanke masa hukuncin jeka ka gyara halinka na tsawon watanni goma sha takwas, kuma an bada umarnin cewa likitoci sun binciki hankalinsa.
Shi dai mutumin mai suna David Scofield, ‘dan shekaru hamsin da haihuwa ‘dan asalin garin Lancaster, an yanke masa hukunci ranar Alhamis a garin Akron. Alkali yaci tarar sa dala dubu ‘daya (Naira 230,000) da kuma kwace duk kayayyakin dake cikin motarsa wadanda suka hada da bindiga, da kuma duk kayayyakin aikin ‘yan sanda da aka kama shi dasu.
An kama Scofield ranar sha uku ga watan Octoba. Bayan daya kunna fitilar da jami’an tsaro ke kunnawa a lokacin da suke tsayar da mutum ga ‘dan sandan gaskiyar, ya kuma shiga gaban dan sandan a can garin Akron.
Scofield dai bai musunta laifin da ake tuhumar sa a aikatawa a kotu na ‘daukar kansa a matsayin dan sandan karya, da mallakar makami ba bisa doka ba har da laifin dagula ko sawa aiyukan jami’an tsaro kafar angulu.
Lauyan Scofield dai yace ya ji dadi, ba’a garkama wanda yake karewa a gidan yari ba.