Emmanuel Adeboyor Zai Bar Cristal Palace Bayan Wasan Karshe Na Zakarun Turai

Emmanuel Adebayor, ya tabbatar da cewa zai bar kulub dinsa Crystal Palace bayan kammala wasan zakarun Turai na karshe.

Dan wasan mai shekaru 23 a duniya, ya rattaba hannu kan yarjejeniya da kulub din a watan Janairu, amma ba kasafai yake ake saka shi cikin wasa ba, kwallo guda kacal ya jefawa kulub din.

Emmanuel yace tafiyar a Crystal Palace tazo karshe a wannan watan na Mayu, amma ba tana nufin karshen sa ba kenan, domin zai ci gaba zuwa duk inda Allah ya kaisahi.

Ya ci gaba da cewa, a koda yaushe yana mai yiwa kulub din fatan alkairi, yana kuma son Cristal Palace ya lashe kofin wasan zakarun Turai da zasu buga.