Babban Kocin ‘yan wasan Swaziland Sihlangu Somnikati yayi alkawarin taka leda bisa dabarun kai hari da zafi-zafi don harar ragar abokan gasar wasan kwallon da za a kara tsakaninsu da Super Eagles ta Najeriya a ranar Talata.
A gasar da ake bugawa don fidda gwanayen da zasu wakilci nahiyar Afirka a gasar FIFA ta cin Kofin duniya a shekarar 2018. Karon farko na wasan da aka fara da shi an tashi kunnen doki a shekaran jiya juma’a.
Idan ‘yan Afirka ta Kudu suka yi kunnen doki ko nasarar bazata a kan ‘yan Najeriya, to sun sami tsallake shingen zagayen tantancewar na gaba.
Wasan dai za a buga shi ne a filin wasa na Adokiye Amiesi-amaka Stadium mai cin ‘yan kallo 40,000 dake Najeriya.
Sai dai hankalin Kocin Najeriyar Sunday Oliseh a tashe yake saboda raunin da dan wasan tsakiyar fili Rabi’u Ibrahim yayi kafin wasan na ranar Juma’a da aka buga.
Oliseh ya zargi dan wasan da boye raunin da ya sami a idon sawu, wanda ya hana shi sakat a wasan musamman ma lokacin da wasan ya yi zafi. Hakan yayi matukar ba wa Mista Oliseh haushi.