Har Yanzu Jam'iyyar APC Na Cigaba da Korafi Akan Daga Zabe

Shugaba Jonathan tare da 'yan jarida suna tattaunawa.

Har yanzu dai kananan maganganu basu kare ba akan batun daga zabe a Najeriya, jam’iyyar APC ta ce akwai wata makarkashiya da Shugaba Goodluck Jonathan ya kulla.

Jam’iyyar APC dai na cigaba da ‘daura alhakin ‘dage zabe a kan shugaba Goodluck Jonathan, domin a cewar sakataren jam’iyyar APC ta kasa Alhaji Mai Mala Buni, a kwai ayar tambaya akan hujjojin da aka bayar. Inda yace, “Tambaya shine a lokacin da yake bayarda da tabbacin ga sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, baiyi shawara da ainishin hafsosin shugabanni na tsaron kasar bane? Har suka tabbatar da cewar bazasu iya bada tsaro ba ko zasu iya bada tsaro, sannan ya bada tabbacin cewar za’a gudanar da wannan zabe kamar yadda aka shirya.”

Ya kuma cigaba da cewa su kansu hafsoshin sojojin kasar Najeriya, sun zauna sun tabbatar wa da ‘yan Najeriya, cewar a shirye suke za’a gudanar da zaben nan kamar yadda ya kamata, amma kuma cikin dan kankanin lokaci suka fito sukace bazasu iya bada tabbacin tsaro a gudanar da zabe kamar yadda aka tsara.

Shikuma Abdullahi Ali Kano, ‘dan kwamatin Kamfe na shugaba Jonathan ya musunta zargin na ‘yan adawa. Inda yace, “duk wani hanyoyin da za’ayi zabe a kasar nan jam’iyyar PDP ta tabbatar da cewa daga duk shirye shiryen da INEC suka farayi tun shekara ta dubu da goma sha hudu har zuwa yanzu, babu abu daya da hukumar INEC ta nema da gwamnati bata bayar ba kan zabe mai zuwa, magana PDP nada hannu kan dage zabe ba haka bane.”

Abin jira a gani shine ko jami’an tsaro zasu iya samun nasarar dawo da tsaro a makonni shida, in anyi la’akari da harin da ‘yan Boko Haram suka kai Gombe, a karshen mako harma suka raba wasu takardun gargadi ga duk wanda ya fito zabe.

Your browser doesn’t support HTML5

Korafin Jam'iyyar APC - 3'04"