Illimi Mabudin Rayuwa

Shugaba Obama da Yara 'Yan Makaranta

Jahar Michigan ta kasar Amurika kan iya zama jaha ta farko da zata bada takardar shaida ga yara ‘yan makarantar sakandire a bangaren ilimin kimiyya, fasaha, aikin Injiniya da kuma kwarewa a harkar Lissafi.

Dan majalisa jahar Mr. John Proos ya bayyanar da hakan a zauren majalisa. Ya kuma kara da cewar a cikin ka’idojin da dalibi zai cika don samun wannan takardar shaidar, sun hada da samar da Kredit 6 a bangaren ilimin kimiyya da lissafi. Yace wannan takar dar shaidar zata ba ma yara damar samun aiki cikin sauki, a kasuwar aiki.

Mr. Proos dai ya kara da cewar, abu mafi matukar mahimmanci a nan shine, masu aiwatar da manufofi yakamata su maida hankali wajen samar ma wadannan yaran yanayi wanda zasu iyayin dogaro da kansu a ko ina, kasancewar samun aiki yazamo wani abun mai wuya.

Ya kuma yi nuni da cewar, wannan shaidar zatasa kamfanoni da sauran ma’aikatuni su zowannan jahar don daukar ma’aikata a kowane irin fanni aiki.

Your browser doesn’t support HTML5

Illmi Mabudin Rayuwa - 1'00"