Illolin Hanyoyin Sadarwa na Zamani ga Ilimi

Ilimi da Kimiyyar Zamani

Bisa ga wani bincike da wani Farfesa na jami’ar Indiana a jihar Pennsylvania, a kasar Amurka, ya gudanar, Farfesa, Luise Almeida, ya tabbatar da cewar hanyoyin sadarwa na zamani wato kimiyya, na da illoli da dama, musamman a bangaren ilimi, da kuma zaman takewar yau da kullum.

Ya kara da cewar a lokutta da dama mutane kan kamu da wadannan abubuwan kimiyar, kamar su kwamfuta, wato nau’ra me kwakwalwa, wayoyin salula, allon zamani da dai sauransu, wanda kuma a kasari mutane basu iya rabuwa da wadannan abubuwan batare da samun wata damuya ta kwakwalwa ba a dalilin sabo da irin wadannan nau’rori.

A bangaren ilimi yana ganin, wannan na’urorin kan dauke ma yara hankali da ba zai barsu su gudanar da karatunsu ba yadda yakamata ba saboda daukar hankali, da yake da, sai ya kara da cewar ma babu kamar idan ance wadannan na’urorin na hade da yanar gizon tafi da gidanka.

A bangaren mu’amalar yau da kullum kuwa, wadannan na’urorin zamanin kan raba kan iyalai, abokai, har dama al’umah idan ba a maida hankali ba, saboda a wasu lokutta sukan raba zumunci, ko kuma sukan kawo nisanta iyalai da masoya, wanda a wasu yanayi iyali basu sanin halin da ‘yayansu ke ciki ko maigida da matarsa, dalilin kowa na kan na’urarsa ba wanda ke da lokacin wani.Don haka yayi kira da al’uma su Ankara da wannan annobar zamanin, wadda zata iya kawo matsalolin da za’a’iya kwashe shekaru da dama kamin a samu shawo kan matsalar.