Jirgin fasinja na kamfanin Alaska Airlines, yayi saukar bazata a filin saukar jirage na birnin Seattle ranar Litinin bayan da ya tashi da wani ma’aikacin lodin kaya makale a ‘karkashin jirgin. Shi dai ma’aikacin ya ‘buge barci ne alokacin da yake lodin kaya a jirgin, kuma jirgin ya tashi da shi batare da sani ba.
A wani rahoto ance matukin jirgin na Alaska Airlines mai lamba 448, ya sanar da cewa yaji karan bugawa daga kasan jirgin alokacin da jirgin ke tafiya a sama, ana kuma jin karan ihu daga ‘bangaren da ma’aikacin ke makale, hakan yasa aka umarci pilot matukin jirgin da yayi saukar gaggawa.
Bayan da jirgin ya sauka lafiya daga tafiyar mintuna 14, an samu ma’aikacin a kasan jirgin. Kamfanin jiragen ya fitar da bayani cewar ma’aikacin ya ‘buge barci ne alokacin da yake zuba kayan fasinja a ‘bangaren ajiye kaya na jirgin.
Babu abinda ya faru da shi wannan mutum, kuma an ‘dauke shi zuwa asibiti domin tabbatar da lafiyar sa.
Kamfanin jirgin dai yace yanzu haka yana gudanar da bincike kan abun da ya faru.