Kulob din Bayern Ya Sami Galaba Akan Donetsk

Dan tsaron gidan Beyern

Kulob din Bayern ya sami shiga kwata final zagaye na hudu a yayin da ya sami galaba kan kulob din Donesk.

Fanaritin Thomas Muller ya biyo bayan dan kankanen lokaci bayan bada jan kati mafi saurin da Olexander ya samu a tarihin wanan gasar a sanadiyar wani fawul cikin mintuna uku.

Jeron Boateng da Franck Ribery sun jefa kwallaye duk cikin rabin lokaci bayan zagaye na farko inda wasan ya tashi babu kwallo ko guda. Muller, Holger Badstuber, Mario Gotze da Robert Lewandoski kuma duk sun kara jefa kwallaye.

Kulob din Bayern ya sami nasarar kaiwa kwata final a gasar zakarun turai zagaye na 11 kuma basu da wata shakka duk da sallamar Kuchers daga kulob din. Sau guda ne kawai aka taba fitar da kulob din German a wasannin gasar zakarun Turai bayan sunyi duro 0-0 a shekara ta 1981.