A cigaba da wasannin kwallon kafa na CAF Champions League, kungiyar kwallon kafa ta Enyimba ta kwashi kashinta a hannu a karawar da suka yi da kungiyar kwallon kafa ta Zamalek ta kasar Masar a wasannin su na rukunin B da aka buga a filin wasa na Adokiye Amiesimaka dake birnin Fatakwal a Nijeriya.
A yanzu dai kungiyar kwallon kafa ta Mamelodi Sundowns ta kasar Afirka ta Kudu ce kan gaba a rukunin B da maki uku, biyo bayan ci 2 β 0 da suka yi wa kungiyar kwallon kafa ta kasar Algeria Entente Setif a ranar asabar da ta gabata.
Kungiyar Sundowns zata marabci kungiyar Enyimba a ranar 29 ga watan Yunin da muke ciki idan Allaha ya kaimu.
Soma wasan na jiya ya sami tangarda a sakamakon ruwan sama mai karfin gaske a birnin na Fatakwal, dan wasan gaba na kungiyar Zamalek ne ya fara jan ragamar wasan inda ya kai wa mai tsaron gida na kungiyar Eyinmba Theophilus Afelokhai harin bazata a cikin minti na bakwai da fara wasan.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya kawo wa duka kungiyoyin biyu cikas, musamman yadda musayar kwallo daga dan wasa zuwa dan wasa ta zama da wahalar gaske saboda ruwan da ya taru a filin yayin da ake gudanar da wasan.
A zagaye na biyu, kungiyra Eyimba ta yi iya bakin kokarinta domin samun dai daito amma βyan wasan Zamalek suka rike wuta inda daga karshe wasan ya tashi da ci daya da babu.