Rashin Mijin Aure Ke Sa Mata Komawa Makaranta

A yau dandalin ya zanta da wata matashiya ne domin irin kalubalen da suke fuskanta daga iyayensu bayan sun balaga kuma basu samun mijin aure ba.

Ita dai wannan matashiya mai suna Asama’u Auwal, cewa tayi kowace Uwa tana so idan ‘yarta ta taso tayi kokari ta samu miji tayi mata aure saboda kada ta jamata abun kunya.

Ta kara da cewa , idan aka ce yarinya ta girma ta kai kimanin shekaru 25, zuwa 30, kowane lokaci iyayen hakalinsu yana kan yarinyar suna kafu kafu da ita, wasu lokuta ma har bincikar jakunkuna da wayanta ma ake yi.

Malama Asama’u, ta ce mafi akasarin mata, a yanzu rashin mijin aure ne yasa suke komawa makaranta ba kamar irin shekarun baya ba zaki ga iyaye babu ruwansu kawai yarinya sai ta kai wani matsayi da suke so a karatu sannan zasu yi mata aure, amma yanzu yarinya zata kai matsayin a babu mijin aure.

Ta ce wani lokaci gaskiya ‘yan mata fakewa sukeyi da a koma karatu amma ba karatun akeyi ba rashin mijin aure ne babu shi yasa ake komawa makaranta.