Masana kimiyya na aiki don kirkiro sabon maganin dafin macizan kasashen yankin sahara na Afirka, kasancewar dubun mutane na mutuwa a kowacce shekara dalilin cizon wadannan macizai masu dafi, wasu masana kimiyya dake Birtaniya ne ke aiki kan maganin da zai rage karfin dafin macizan.
Dakta Robert Harrison, na makatarantar Liverpool School of Tropical Medicine, yace duk shekara macizan dake kasashen sahara na kashe kusan mutane dubu talatin da biyu.
Dakta Robert ya cigaba da cewa baya ga kashe mutane, sauran wadanda suka rayu daga cizon macizan kusan mutane dubu ‘dari, suna samun nakasa inda wasu basu iya tafiya, wasu kuwa sun gurgunce.
A yanzu haka maganin da ake amfani dashi wajen kashe dafin, ana yinsa ne da dafin macizan, yana ‘daukar lokaci kafin a hada shi, gashi da tsadar gaske kai dole ne ma a ajiye shi cikin sanyi.
Maganin dafin da masana kimiyya ke kokarin hadawa a makarantar Liverpool, ana yin sane saboda Najeriya, kuma yana da saukin farashi da aminci.