Sabuwar Mota Mai Iya Tashi Sama Kamar Jirgin Sama

FILE - The AeroMobil 3.0 is pictured during its world premiere at Hofburg Palace in Vienna, October 29, 2014.

AeroMobil wata mota ce da zata iya tafiya a sararin samaniya kamar jirgin sama. An kera ta, ta yadda zata iya amfani da kayayyakin motaci dana jiragen sama, wadda ta bude kofa ga wata kafar yin tafiye tafiye na yau da kullun. Kamar yadda take mota zata iya shiga duk inda motoci ke shiga, tana amfani da man fetur, kuma za’a iya tuka akan hanyoyi kamar sauran motoci. Haka zalika a matsayinta na mai tafiya a sama kamar jirgin sama zata iya sauka a kowanne filin saukar jirage na duk fadin duniyar nan. Haka kuma ma iya tashi da sauka kan ciyawa ba sai kan titi kadai ba.

Ita wannan mota da yanzu haka aka kera mai suna AeroMobil ana cigaba da ingantata.

A yanzu dai an gama kera wannan mota, kuma tun a watan oktaban shekara ta 2014 aka fara gwajin a samar kamar yadda jirgin sama ke zirga zirga.

An kera AeroMobil 3.0 da abubuwa da dama wanda suka hada da gangar jiki, fuka-fukai da tayoyi. An kuma kera ta wasu fasahohi da jiragen sama ke dasu.

Shugaban kamfanin AeroMobil Juraj Vaculik ya bada karin bayani akan kamfanin da makomarsa, da irin kalubalen da zasu fuskanta kafin su cimma burin fitar wannan motar kasuwa a shekara ta 2017, idan Allah ya kaimu.