Shekau Yayi Barazanar Kawo Cikas Ga Zabe Mai Zuwa

UNGA

Sanarwar fefen bidoyo da Abubakar Shekau shugaban kungiyar Boko Haram, ya fitar ta barazanar kawo cikas a zaben watan gobe ya zama sabon batu da ‘yan takara ke magana akai, musammamma na yankin arewa maso gabas.

Maganar yiwuwar zaben a ranar ashirin da takwas ga watan Maris, ‘yan takara basu sami sabani ba a duk jam’iyyun da wakilin mu Nasiru Adamu ya zanta dasu. Sun nuna sadaukarwa ce kadai zata iya ceton demokaradiyyar daga rugujewa.

Dan takarar PDP na Borno Muhammad Imam, yace matsalar tsaron na iya nasaba da halin ‘yan siyasa. Ya kuma yi kira ga duk wani ‘dan siyasa dake da hannu don neman abin duniya ko mukami, yayi wa Allah ya duba kansa da iyalansa, in wannan abun bai shafeshiba yana shafar ‘yan uwan wadansu mutane.

A nasa bangaren dan takarar APC a Gombe, Inuwa Yahaya, yana ganin ko da batun fitinar yaki karewa, inda yace, “Duk wanda yazo ya kawo barana ta dabam, ina ganin yana yi ne domin biyan bukatun kansa, da yardar Allah wannan bai kamata ya karya gwiwar kowaba, ya kamata a fito, domin a ina ne ba’a yin barana. Ka fita zuwa sana’a an dakile ka, ka fita zuwa gona an dakile ka, ka fita zuwa massallace an dakile ka, ta ko’ina an cimma dan Najeriya.”

Abin da ya fito dai a wannan karon shine sojoji dai sun nemi maye gurbin ‘yan sanda, wajen nuna yiwuwa ko jinkirta zaben, musammamma, wajen tabarbarewar lamarin tsaro.

Your browser doesn’t support HTML5

Barazanar Shekau Ga Zabe Mai Zuwa - 2'30"