Shugaban Miyatti Allah Yayi Kira Ga Fulani Matasa

Shugaban Miyatti Allah yayi kira ga matasan fulani a game da babban zabe mai zuwa

A yayin da babban zaben Najeriya ke karato wa, shugabannin al'umai daban daban na kokarin yin kira da fadakarwa ga mabiyan su a wurare daban daban a duk fadin kasar.

Wakilin sashin hausa na muryar Amurka Mustapha Muhammadu Batsari yayi hira da shugaban fulanin jahar Niger wanda ya kira taron masu yada labarai kuma yayi kira ga al'umar fulani musamman matasa ya gargade su da kuma yin karin haske a game da babban zaben kuma yayi magana kamar haka.

"Ina kira gare ku matasa dan Allah kar ku sake ayi anfani daku a matsayin 'yan bangar siyasa, kar ku yarda a rude ku da kudi ko kayan shaye - shayen da basu da anfani domin kawo rudani a lokacin zabe".

Daga karshe kuma yayi karin bayanin cewar kungiyar su ta Miyatti Allah ba kungiyar siyasa bace, dan haka kowa na da 'yancin zaben wanda yake ra'ayi, kuma bugu da kari zasu yi zaben su ba tare da matsala ba.