WASHINGTON, DC —
Wata mai suna Blessing Edeh, ta dabawa saurayinta wuka a ciki wanda yayi sanadiyar sa na shekawea barzahu a yanki Lekki a jahar Lagos.
‘Yar shekaru ashirin da hudu da haihuwa Blessing ‘yar assalin jahar Akwa Ibom, tace saurarin na ta mai suna Ebong, yana kishin tane kuma ita bata yi wani nadama ba saboda in ji ta fada ne tsakanin mutane biyu.
Kamar yadda jaridar Punch, ta ruwaito tace saurarin na Blessing da shekari talati da ukku da haihuwa yana saune ne dare da budurwar tashi a muhallinta baya da suka amince za suyi aure.
Abun da ya jawo fada tsakanin su shine a lokacin da saurayin ya dawo daga aiki sai ya bukaceta da ta dafa masa abinci ita ko ta ki sai cha char baki daga bisani abun ya kai ga fada inda ta ta dabamasa wuka a ciki.