Arzikin ji da Gani da lafiya da Wadatar Zuci

Sana'ar Tuwo

Arzikin ji, gani, lafiya, da wadatar zuci, sune babbar kyauta da Allah keba wanda yaso, don haka ashe yakamata mu dogara gareshi kuma munema gareshi ba ga wani dan'adam ba. Hajiya Aisha, mai tuwo, ta bayyanar da kanta a matsayin matar da ta fuskanci wasu halaye a rayuwa da sukasa ta kara fahimtar me cece duniya.

Ta samu kimani wasu shekaru tana wannan sana’ar wadda bada ita ta far aba, amma a yau tana kara gode ma Allah, da yasama sana’ar albarka, ganin yadda take daukar dawainiyar ‘yayan da Allah ya basu guda fiya ta kuma tallafama mai gidan ta a inda bashi da. Takan taimaka wajen biyan kudin makarantar yaran da dai sauransu.

Ta kara da cewar shi dai dan'adam idan bai raina sana’a ba, to lallai zai iya kaiwa ko ina a rayuwa, sai dai babban abun cewa a nan shine yakamata ace kowane mutun yasa tsoron Allah, a duk abun da zai aiwatar kamin ya kaiga yi, don wannan shine kawai zaisa mutane su kara jawo hankalin wasu marasa sha’awar kowane irin kasuwanci, su shiga don suma a dama da su.

Ashe kuwa kaga wani bai iya isanma kanshi batare da taimakon wani ba a rayuwa, don haka jama’a su bada himma wajen neman na kai da dogaro ga Allah ba wani nakaba.