WASHINGTON, DC —
Bayan jefa kwallon farko ta nasarar da kulob din Chelsea ya samu a kan kulob din Tottenham inda wasan ya tashi 2 – 1, kaftin din Kulob din Chelsea John Terry, ya sami 'yan rakiyar dan tsaron gida Petr Cech da dan wasan gaba wato Didier Drogba zuwa stadium din Wembley, dake tsakiyar birnin London, inda Jose Mourinho ya daga kofin .
“Wannan ya bamu dandanon abinda muke sa ran yi a karshen wannan kakar wato daga kofina da dama inji Mourinho”.
Wannan shine na farko wato idan muka waiwayi baya a shekara ta 2004 zuwa 2005 kuma abin lallai ya shafi tawagar kwarai da gaske kuma yana iya shafar sabuwar tawagar mai tasowa.
Mourinho dai na ganin wannan a matsayin wani sabon zamanin kulob din na chelsea.