Ya Kashe Shi da Zoben Asiri

Mazauna unguwar Omilabu,Odinjo a garin Ibadan, dake cikin jahar Oyo,sun tsinci kansu cikin halin makoki bayan rasuwar wani Mumini Murtala, da shekaru 40, da haihuwa.

Shi dai Mumini,ya rasu ne sakamakon bugun sa da wani Yusuf, wanda ya kasance dan mai gidan da shi Mumini ke haya a cikin ya yi masa da wani zobe na asiri.

Matar mamacin Shakirat Murtala, tace mijinta da 'ya'yan mai gida Yusuf Adegbayi da kaninsa Habeeb, sun fara cha char baki ne sakamakon rufe kofar shiga cikin gidan da suke haya wanda daga bisani ta kai ga fada tsakanin mutanen wanda yayi sanadiyar mutuwan Mumini.

Wadanda ake tuhuma da kisa sun ranta ana kara amma mahaifinsu wanda shine mai gidan yana hannun hukuma.