Ya Take Ne Matasa

Bana Bakwai

A wannan makon shirin Bana Bakwai ya leka jahar Niger Najeriya ne inda ya tattauna da matasa domin jin irin nasu salon maganar.

Umar Isah Junior ya bayyana mana cewar idan suka ga tsaleliyar budurwa a hanya , sukan ce ga wani shago nan kuma babu yadda zaka gane idan ba daga yankin su ka fito ba. A wannan lokaci idan wani daga cikin su bai ganta ba, yana iya tambaya kanti ko gwanjo?.

Idan ta hadu sai a ce kanti, idan kuma bata hadu ba amsar itace gwanjo!

Da muka koma jahar Kano kuma, wani matashi ya ce idan kana cikin jama’a kuma kana maganar wani wanda bakasan yana wurin ba, ko kuma wani dan’uwansa ko abokinsa ba, da zarar kaji ance sa madubi to lallai kasan akwai wani Kenan, hakan zai sa ka canza zancen ko kuma ka bar Magana.