Yakin Neman Zaben Shugaban Hukumar FIFA

Sepp Blatter Shugaban Hukumar FIFA

Shugaban hukumar FIFA Sepp Blatter, ya bayyana cewa yana yakin neman a sake zabar sa a zabe mai zuwa, bisa ga aikin da yayiwa hukumar FIFA har na tsawon shekaru 40, kuma bazai fitar da rubutattun manufofinsa ba.

Shi dai jami’in ‘dan shekaru saba’in da tara da haihuwa, na fuskantar kalubale a zaben da aka shirya yi a zauren majalisa a Zurich 28 da 29 ga watan Mayu, ana kuma kyautata tsammanin shine zai samu nasara a zaben, Blatter dai yaki fadin manufofinsa ko aikin da zaiyi idan aka zabe shi a kashi na biyar.

A wani taron manema labarai blatter yace, “manufofi na shine aikin da nayi a shekarun da suka wuce a FIFA, yanzu haka na cika shekaru arba’in a FIFA, kuma yanzu haka na cika shekaru goma sha bakwai ina shugaban tar wannan hukuma, wadannan sune manifofin na.

Shugaban na FIFA dai yaki amincewa da wani zaman muhawara da abokin karawarsa Ali Bin Al Hussein, wanda shine mataimakin shugaban FIFA daga kasar Jordan.

Amma ‘yan takarar hudu zasuyi magana a gaban ‘yan majalisun hukumar kwallon kafar Turai a can Vienna ranar Litinin da Talata.