'Yan Banga Sun Ce Zasu Iya Tarwatsa 'Yan Fashin da Suka Addabi Jihohin Arewa Maso Yammacin Najeriya; Mukarrabin Laurent Gbagbo Yace Ba Ya Da Laifi - 27/3/2014

NAJERIYA - Shugaban kungiyar ‘yan bangar Najeriya, Ali Sokoto, yace zasu iya magance ‘yan fashin da suka addabi Zamfara, Katsina da Kaduna in aka ba su gudumawa. An bayyana cewa ‘yan fashin sun yi sansani a cikin dazuzzuka na Katsina, Zamfara, Kaduna har ma da Kebbi, inda suke yawaita tare hanyoyi su na fashi wa mutane tare da aikata ta’addanci a kan wasu kauyuka da garuruwa.

NAJERIYA - Direbobin kamfanin Dangote sun yi wani gangami suka rika tsare motocin kamfanin a hanyoyin Lagos yau alhamis. Direbobin sun gabatar da korafe korafen cewa mutanen da aka ba shugabancin kamfanin su na kwararsu, ba su biyansu hakkinsu kamar yadda aka ce za a biya su.

IVORY COAST - Wani tsohon shugaban matasa na kasar Ivory Coast da ake zargin yana da hannu a kashe kashen da suka biyo bayan zaben shugaban kasa na 2010, ya ki amsa wannan laifi yau alhamis a lokacin da ya bayyana a gaban kotun buin kadin manyan laifuka ta duniya. Charles Ble Goude, wanda ya bayyana yana murmushi ya fadawa kotun dake birnin Hague cewa ba ya tsammanin za a kama shi da wannan laifi na cin zarafin bil Adama.

MALAYSIA - Hotunan tauraron dan Adama na kasar Thailand sun nuna karin tarkacen da watakila sun fito ne daga jirgin saman fasinjar kasar malaysia da ya bace, amma kuma an sake jinkirta farautar jirgin ko tarkacensa a saboda rashin kyawun yanayi. Hukumar binciken sararin samaniya ta Thailand ta fada yau alhamis cewa daya daga cikin taurarin dan Adama nata ya hango wasu abubuwa kamar guda 300 su na yawo kan ruwa a yankin kudancin tekun Indiya, tarkacen da girmansu ya kama daga mita biyu zuwa 15.

Your browser doesn’t support HTML5

Labaran Najeriya, Afirka Da Duniya A Takaice - Alhamis - 3'00"