Yaran Da Suka Rasa Iyayensu A Sanadiyar Rikicin Boko Haram

Yara 'Yan gudun hijira a makarantar firamare a Damare, Yola1

A cigaban tattaunawar Ibrahim Alfa Ahmed da wasu yara kanana ‘yan kasa da shekaru goma wadanda suka rasa iyayensu a sakamakon rikice rikicen da ‘yan kungiyar Boko Haram ke haddasawa, yaran dai na zaune a sansanin ‘yan gudun hijira dake Jola jihar Adamawa.

Yaran sun gayawa Ibrahim, cewar suna samin abinci a wannan sansani da suke kuma ana raba musu kayayyaki da sauran abubuwan da suke bukata, duk da yake yaran suna jin dadin zaman sansanin amma sunfi son su koma gidajen su, ko kuma wani guri na da bam.

Sun kuma bukaci mutane da su taimaka musu da duk abinda Allah ya hore kamar da kudi, kayayyakin sawa, abinci da sauran abubuwan bukata na rayuwa kasancewar halin da suke ciki. Batun makaranta kuwa suna zuwa, harma akwai wani shiri da aka bude musu ga masu son zuwa neman ilimi a wasu gurare na daban, inda zasu cike wasu takardu domin daukarsu zuwa wasu makarantu.