A shirinmu na nishadi a yau Dandali ya sami bakuncin Isma’il Nabba Afakallah daraktar hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano inda yace hukumar an durata ne ta tace dukkan abubuwa da suke na fasaha wadanda suka jibanci rubutu, ko fina finai ko kuna abubuwa da suke da dangantaka da irinsu.
Yace ba hukuma ce na tace fina finai ba kawai ba hukumace na tace fasaha irin ta zamani da sauransu, shi yasa zaka internet café suna ciki masu daukar hoto suna ciki masu gidajen wasani suna ciki zannan masu dab’I suna ciki saboda duk abubuwa ne na fasahar zamani.
Isma’il Nabba Afakallahu yace yanzu haka hukumar ta fito da tsare tsare na ganin cewa masu harka fina finai sun bi kaidojin da hukumar ta shinfida dangane da irin siturun da suke sawa.