WASHINGTON, DC —
An gano daya daga cikin ‘yan makarantar mata na Chibok,da ‘yan kungiyar Boko Haram suka sace shekaru biyu da suka gabata.
An gano wannan yarinyar ne a wani kauye dake tsakanin wani gari da ake kira Bali da dajin Sambisa a lokacin da ‘yan Kato da Gora da rundunar Sojoji suka shiga dajin Sambisa domin gudanar da sintiri.
Tuni dai aka mika wanna yarinya ga jami’an tsaro dake karamar hukumar Dambuwa, domin ci gaba da gudanar da bincike a kanta.
Malam Afagu, daya daga cikin jami’an sintirin da suka gano wanna yarinya kuma dan garin Chibok, ya tabbatar da, cewa ya ga yarinyar da idon sa har ma sun kai ta yarinya ga iyayenta kafi amika ta ga jami’an tsaro.