An Kama Tsohon Daraktan Kulob Din Spaniya Da Abokan sa Biyu

Jami’an tsaro sun kama tsofaffin daractoci uku na kulab din spaniya.

Kotun yankin arewacin Navarra tace an kama tsohon shugaban kulabdin kwallon kafar da wasu tsaffin ‘yan kwamitin zartarwar kulab din su biyu.

Kotu ta bayyana cewa jami’an tsaro sun kama Miguel Archanco, Txuma Peralta da Vizcay ne a yau alhamis kuma zasu gurfana a gaban alkali cikin awoyi 24. Ana kyautata zaton za’a cigaba da tsare su ukun har zuwa ranar juma’a.

Dalilin kama su ya taso ne a sanadiyar wani binciken da jami’an tsaro suka gudanar akan layar zanar da wasu makudan kudi har yuro miliyan 2.4 wato kwatankwacin dala miliyan 2,746 kenan daga aljihun kulab din a tsakanin watan Nuwambar shekara ta 2013 zuwa watan yulin shekara ta 2014.

Daraktan kulab din na yanzu wato Pedro Baile Osasuna ya amince da kwamitin binki da suyi bincike a kan lamarin domin mayar wa da kulab din kudin sa.

​##caption:Sunyi sama da fadi da kudade.##