An Tuhumi Yaro Mai Shekaru 14 Da Laifin Kisa

Russia Opposition Trial

An tuhumi wani yaro ‘dan shekaru 14 da haihuwa da laifin yunkurin kisa bayan da ya soki wata yarinya da wuka.

Lauya mai gabatar da kara na jihar Colorado ne ya gurfanar da yaron a ranar Litinin, laifukan da ake tuhumar yaron kuwa sun hada da laifin kai wa yarinyar hari, da laifin ‘daukar makami a harabar makaranta ba tare da izini ba, tuhumar dai ta biyo baya ne bayan dya caka wa yarinyar ‘yar shekaru 14 wuka a satin daya gabata a wata makarantar firamare dake yankin garin Denver.

Jami’ai dai sunce ma’aikatan agajin gaggawa sun ‘dauki yarinyar zuwa asibiti a jirgi, bayan faruwar lamarin amma yarinyar ta rayu.

Mai gurfanar da ‘karan dai yace an shigar da karan ne bisa bin ka’idar shari’a, yanzu haka kuma yaron daya aikata laifin na tsare a gidan kangararru.