Kasancewar babu wani mai alfahari kan ‘ya ‘yan da basu da tarbiya a wannan rayuwa, dalilin haka ne muka ji tabakin farfesa Sama’ila Zango, wanda ke masanin ilimin halayyar dan adam kuma mai sha’awar nazari da bincike akan harkokin al’umma yana kuma koyarwa a jami’ar Bayero ta Kano.
Farfesa Sama’ila, na ganin ita al’amarin haihuwa abune na Allah, domin shike bayarwa amma shi ‘dan Adam ya banbanta da sauran dabbobi, don ‘dan adam na bukatar a tarbiyar da shi akan abubuwa na yau da kullun, haka nan yana bukatar tarbiyar yadda zai gudanar da rayuwar sa, idan kuwa aka sami rashin yin hakan to za’a ga cewa mutum bashi da al’ada irin ta ‘dan adam domin rashin kyakykyawar tarbiya.
Yana da kyau kuma wajibine idan mutane suka haifi ‘ya ‘ya suyi musu tarbiya ta gari. Farfesa ya bada missali da wani hadisi da yake nuna kowanne mutum mai kiwo ne, maigida an bashi alhakin kiwon gidan sa wanda ya hada da matan sa da ‘ya ‘yan sa, kiwon kuma ya hada da tufatarwa, ciyarwa, da muhalli, rashin yin hakan na haddasa gurbacewar tarbiya ga yara da gida baki daya.
Yaran da suka taso batare da sanin mai nene kauna daga gurin iyayensu, ta ina kuwa zasu sami kauna da tausayi ga sauran al’umma, hakan na haddasawa irin wadannan yara idan suka sami dama da zasu cusgunawa al’umma domin cire haushin dake cikin zukatansu to zasuyi. Kamar dai yadda hausawa ke cewa, da haihuwar yuyuyu gwanda haihuwar ‘da daya kwakwkwara.