Dan Sandan Boge A Afirka Ta Kudu

'yan sandan Afirka ta Kudu a kan aiki

Wani labari mai kamada al’mara ne ya auku a Afirka ta kudu inda wani tsohon mai laifi ya tsere daga wani babban gidan yari ya nufi wani ofishin yankin na rundunar sandan kasar yace dasu an sauyawa masa wurin daga helkwatar rundunar ‘Yansanda zuwa wnnan ofishin, ya kuma bayyana kansa a matsayin shine kaftin Mailula.

Manya a wannna caji ofis din suka karbe shi ba tareda sun gudanar da wani bincke ba, kuma ya ci gaba da aiki a wannan ofishin har na tsawon shekaru uku, inda har akayi masa karin girma ya zama detective watau kwararru a fannin bincike. Babu fashi yana zuwa wurin aiki ko wace rana, sanye da kayen aikinsa da bajin sa wato lambar da jami’ai ke sanyawa a gaban rigarsu.

Abokan aikin nasa ne suka kamashi kuma ya samu ya kubuce bayan kwana biyu ya shiga ‘buya.

Acewar mai magana da yawun ‘yan sandar kasar, Kanal Ronel Otto, yace, “idan har muka tabbatar da wannan zargi ya zamanto gaskiya, tabbas zai zamanto abin kunya ne a garemu.”

An bayyana ainihin sunan wannan dan sandan kariya ko na bogi da cewa shine Alex Matsobane Maake. Dama can yana zaman fursina ne saboda an sameshi da laifin fyade, sata, harma da laifin guduwa daga gidan yari a babban birinin Pretoria a shekara ta 2012.

Ya dai bayyana ne a ofishin ‘yan sandan na yankin Limpopo, yace an aiko shine daga babban ofishin ‘yan sanda na kasa, amma babu wanda ya duba tarihin shi, haka suka barshi ya fara aiki.

Wata jaridar kasar da ake kira City Press, tayi hira da wasu ‘yan sandan da suka san shi wannan mutumin, wasu daga cikin su sunce sunyi mamaki, wasu kuma nacewa tunda suka fara aiki dashi da akwai wani abu da bai kwanta musu ba gameda dan sandan nan na kariya wanda ya radawa kansa sunan Kaftin Mailula.

Wani da yayi magana da jaridar City press, yace “ya dade yana rufta kowa, ciki harda shugabanninsa. Ya sami aljannar duniya sai holewa yake yi, yana tuka motoci masu dan Karen tsada da tilas sun dara albashinsa, amma duk wannan bai sa shugababbinsa suka nuna wata shakka ko bincike gameda keftin Mailula.

Kamar yadda muka gaya muku dai Maake, wand a shine daya daga cikin ainihin sunayensa dai har karin matsayi ya samu a garin na Seshego, amma wasu daga cikin abokan aikin sa na kokawa kan yadda yake tafiyar da aikinsa, wanda yake sa suna faduwa a gaban shari’a kan bincike binciken da ya gudanar.

A wannan dambarwar sai tayu shi Maake bashi da lambar aiki, saboda haka tana yiyuwa yana aikine ba tare da ana biyansa albashi ba.

Yanzu daya daga cikin abubuwa da suke daurewa ‘Yansanda kai shine kan ko me yake yi lokacinda yake fita da motocin hukuma dauke da makamai saye da kayan sarki, inji majiyar.

Wannan lamari dai yazo karshe ga Maake, inda dubun sa ta cika aka kama shi aka daure, amma kash, bayan kwana biyu kurum da kamashi sai sake guduwa, kuma har zuwa yanzu ba’a san inda yake ba.

Mai magana da yawun ‘yan sandan dai Otto ya tabbatar da cewa ‘yan sanda zasu tuhumeshi da laifin zama ‘dan sandan karya dakuma guduwa daga inda aka tsare shi. Ya kuma ce ana binciken wannan zargi.