Akan Batun tsige wakilan da basa yiwa talakawa aikin daya kamata, Barista Aminu Gamawa, yayi mana karin haske kan hanyar da mutane zasu bi domin neman a cire su daga kan mukamansu.
Kundin tsarin mulkin Najeriya, ya tanadar da yadda ‘yan kasa zasu zabi shugabanninsu da wakilansu, haka zalika shi wannan tsarin mulki ya kuma tanadar da yadda su jama’a idan basu yarda da wakilcin da shugabanninsu keyi ba, akwai hanya da zasu bi domin ciresu daga mukamansu na wakilai.
A sashe na sittin da tara na kudin tsarin mulkin Najeriya, na shekara ta dubu daya da dari tara da casa’in da tara 1999, ya tanadar da cewa idan har ‘dan majalisa na jiha ko na wakilai, ko sanata ya zamanto cewa baya aikin da aka zabe shi ko kuma mutanen mazabarsa sun ga cewa bai dace ya wakilce su ba saboda abubuwan da yakeyi ba dai dai bane. Zasu iya rubutawa hukumar zabe mai zaman kanta takardar kai, idan aka samu rabin mutanen dake mazabar suka cika takardar kai, suka rubuta sunayensu kuma suka sa hannu cewa suna bukatar hukumar zabe mai zaman kanta da ta gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a domin cire wannan wakili.
Hukumar zabe zata duba wannan takarda da aka kawo a gabanta, zata kuma tantance idan har tabbas rabin mutanen da sukayi rijistar zabe a wannan mazabar basu amince da wakilinsu ba, to zata gudanar da zaben jin ra’ayin jama’a idan har mutane kashi hamsin cikin dari suka kada kuri’ar basu yarda da wakilin ba, to hukumar zabe zata rubuta wata takarda zuwa majalisar dokoki ko ta wakilai, daga ranar kuwa shi wannan wakili zai rasa mukamin sa.
Dalilin wannan tsari kuwa shine domin akwai mutane dayawa wanda ke yiwa jama’a alkawuran karya daga baya in an zabe su ba zasu cika wannan alkawarori ba, akwai kuma mutane da za’a zaba domin su wakilci jama’ar su amma sai su watsar da al’amuran da suka shafi jama’ar su suna yin abinda da sha musu gaba kawai. Saboda kawo karshen hakan, kuma ga duk wanda aka zaba yasan cewa yana wakiltar jama’a ne ba kansa ba, shi yasa aka baiwa jama’a wannan dama.