Karin Wa’adin Katin Zabe A Najeriya

Na'urar Karanta PVC

Hukumar zaben Najeriya na nuna alamun kwantar da duk wani korafi ne kan rashin raba adadi mai yawa na katin shaidar zaben, inda a yanzu haka ne take cewa a wasu sassa ma tayi nasarar raba fiye da kashi casa’in cikin dari.

Sabuwar ranar ashirin da biyu ga watan nan na rufe bada rijistar, zai zamanto kwana shida ne kawai kafin ranar babban zaben na shugaban kasa da ‘yan majalisun Najeriya.

Jami’in labarun shugaban hukumar zaben Kayode Idowu, na nunin nasarar gwajin amfani da katin tantance masu kada kuri’a, dayake nuna ingancin rijistar zaben. Jagororin jam’iyyun dai na nuna gamsuwa ga karin wa’adin da nuna kwarin gwiwar samun nasara a babban zaben.

Kan umarnin yiwa wata kungiya Young Democratic Party rijista, da sanya ta a takardar kada kuri’a daga babbar kotun tarayya, hukumar zaben dai tace bata samu bayanin hakan daga kotun ba balle ta dauki wani mataki akai.