Kungiyar matasa masu goyon bayan Janal Buhari sun koka kan ganin yadda jam'iyyar PDP take amfani da karfin mulki domin samun biyan bukatunta.
Kungiyar dai bata ga laifin hukumar zabe mai zaman kanta INEC, kasancewar kungiyar dai tabi abin da suka kira doka da oda wajen dage babban zaben.
Shin ko kungiyar da sauran magoya bayan Janar Buhari sun fara razana ne kan dage zaben, shugaban kungiyar na kasa Alhaji Adamu Nguru, yace ko kusa, domin a tarihi akwai kasashe da aka dage zabensu, dagewar ta zamewa jam'iyyar hamayya da kasashen alheri.
Daga nan ne yayi barazanar cewa muddin aka kasa gudanar da zabe ranar 28 ga watan Maris kamar yadda aka yi alkawari, to kungiyar zata tafi kotun duniya domin neman a bi musu hakinsu.
Saurari cikakken rahotan.
Your browser doesn’t support HTML5