Yanzu Haka dai yan kasuwar da hare-haren Boko Haram ya shafa, a arewacin jihar Adamawa sun bukaci da akai musu dauki, ganin yadda suke cikin mawuyacin hali.
Hare-haren dai ya durkusar da harkokin kasuwanci musamman a shiyar arewa maso gabashin kasar, batun da yasa yan kasuwar ke yin kira da a kai musu dauki.
Kama daga garin Madagali, Michika, Maiha, Gombi dama yankin Mubi dake zama cibiyar kasuwancin jihar Adamawa, dubban ‘yan kasuwane hare-haren ‘yan Boko Haram ya shafa, kama daga asarar rayuka da dukiya lamarin daya sa yanzu wasu dake gudun hijira a Yola, soma sana’ar sayar da shayi dama wasu kananan sana’o’i don neman abin sawa a baka.
Wakilin mu Ibrahim Abul’aziz, ya tambayi Alhaji Ibrahim Mohammed mataimakin shugaban kungiyar hadakar kungiyoyin ‘yan kasuwa na arewacin Najeriya, shin ko yaya hare-haren ‘yan Boko Haram ke shafar harkar kasuwanci da kuma tattalin arziki? Ya kumace, “Domin yawanci mu dama, harkokin kasuwanci a arewa ‘yan tiredar a kasa a sayo azo a karkasane hakan nan acikin shaguna ana sayar da shi, to sai ya zamanto rashin kwanciyar hankalin nan yazo ya kawo mana matsala, duk wata masifar da kaji ta faru musamman a yankin jihar Adamawa, Taraba da Yola, zaka samu yawancin asarar na fadawa ne kan ‘yan kasuwa.”
Kawo yanzu dai gwamnatin jihar Adamawa ta kafa wani kwamiti na mutane goma sha bakwai don duba irin asarar da akayi sakamakon wannan matsala ta ‘yan Boko Haram, Alhaji Haruna Mafuro babban sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar ya bayyana irin ya bayyana irin matakin da aka dauka. Inda yace yanzu haka zasuje su duba suga irin ‘barnar da akayi, sai kuma a zauna asan irin ‘barnar sannan a taimaka.
Fata dai shine Allah ya kawo karshen wannan futuna dake hana mutane barci.
Saurari rahotan Ibrahim Abudul’aziz.