Kwesi Nyantaki ya yi hangen cewar wasan karshe da za’a buga tsakanin Najerya da Ghana a gasar matasan Afirka a Senegal a matsayin somin tabi.
Kulob din Black star na kasar Ghana dai ya fafata da takawaran sa na kasar Afirka ta kudu ranar litinin da ta gabata a yayin da Najeriya kuma ta lallasa mai masaukin baki da ci 3 – 1 a lokacin bude wasan.
Ghana dai tana fatan sake komawa matsayin ta na da a lokacin wasan ‘yan kasa da shekara 20 na WAFU da akayi a shekara ta 2009.
Kuma shugaban na Ghana Football Authority wato Kwessi Nyantaki, yayi imanin cewa kulob din Black Starlights da takwaran nasu na Najeriya sunfi zama wadadn da suka fi kowane kulob karfi a wannan gasar.
“Ina hangen yadda wasan Najeriya da Ghana zai karke” a cewar Kwesi a wata hira da yayi da gidan radion Happy FM.