Muhimmancin Ilimi Mai Zurfi ga Matan Aure

Mulher tenta aliviar criança afectada por gás lacrimogénio durante confrontos entre a polícia e vendedores ambulantes  em Harare no Zimbabué.

Kamar yadda a wannan zamani namu ake ganin ilimin mata mai zurfi na kawo matsala ga zaman gida da aure baki daya. Wasu dayawa na ganin zurfin ilimin mata shine ke sanya su, ganin kansu daya da mazajensu koma sun fi su.

Ba duk matan da suka yi ilimi mai zurfi ba ne ke daukar kansu da ganin cewa sun fi mazajen su, inji Hajiya Turai Yar'Adua, matar tsohon shugaban kasar Najeriya, kuma tsohuwar malamar makaranta.

Hajiya Turai, dai na ganin idan har aka ilimantar da ‘ya mace to an ilimantar da al’umma baki daya, idan aka duba zamantakewar zaman gida, to tabbas za’a ga banbanci zakanin matar dake da ilimi dakuma matar da bata da shi, koda ta bangaren taimakawa yara da aikin gida mace mai ilimi ka iya taka rawar gani, maras ilimi kuwa ba lalle bane ace ta taimaka musu da komai ba.

Yadda dai ake ganin cewar don mace nada ilimi zata rinka daukar kanta kamar namiji, a ginin Hajiya Turai ba haka bane, mata masu ilimi sunfi hankali domin sun san yakamata da iya kiyaye zamantakewa da zaman aure. Kuma duk yawancin auren dake mutawa in aka duba za’a ga cewa mijin da matar basu da wani ilimi, ire-iren wadannan hadi na kawo mutuwar aure da wuri fiye da auren masu ilimi a wannan zamani.

Ilimin mata abu ne mai kyau ga al’umma, kasancewar su ke rainar yara da kula da duk wani ayyukan makarantar su alokacin da mazaje ke neman abinda za’a saka a baka.

##caption:'Yan makaranta mata da suka kubuta da daga sakadaren gwamnati na Chibok a wurin ganawa da Goodluck Jonathan 22, ga Yuli 2014.##