Hukumar hana fataucin muyagun kwayoyi ta Najeriya, wato NDLEA, ta sake cafke wani ma’aikacin kamfanin zirga zirgan Jiragen sama na Arik, Ikechukwu Chibuzor Oliver, da take zargin sa da hannu a safaran hodar Ibilis mai nauyin 20gm zuwa kasar Ingila.
Hukumar, tace Oliver, ya amsa laifin, ya kuma ce za’a biya shi Naira miliya 1 da dubu 200, akan jakunkuna ukku dake dauke da hodar kowace jaka na zaman Naira dubu 400 ne.
Oliver, dai na aiki a bangaren masu jigilar, abinci ne akan jirgi, kuma ya taimakawa Chika Egwu Udensi, ne wanda yake cikin ayarin masu hidima da jama,a a cikin jirgin, ya dora masa hodar akan jirgi mai lambar W3101, da zashi kasar Ingila.
Isar jirgin Ingila, keda wuya sai ma’aikatan tsaro a filin jirgin saman Hearthrow, a birnin London suka cafke shi.
Oliver, dai yace Udensi, ya jefa shi cikin wannan muguwar sana’a ta fatauci kwayoyi.