Rashin Daukaka Fasahar Matasa Na Damun Shugabannin Matasa

Wasu Kayan kere-kere

Rashin daukaka fasahar wasu yara kanana mata su 4, ‘yan shekaru 14-15 da haihuwa, wadanda su ka kirkiro janaraton bayar da wutar lantarki, mai mafani da fitsari a matsayin makamashi maimakon man fetur da ke gurbata muhalli; ya sa wani Shugaban matasa a Najeriya yin Allah wadai da halin ko-oho na bangaren gwamnati da bangare mai zaman kansa.

Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewacin Najeriya Alhaji Abdul Isiak, ya ce kamata masu hannu da shuni da kuma hukumomi a Najeriya, su daina rikon sakainar kashi ma hobbar matasan kasar, su tashi haikan su daukaka fasahar ‘yan matan nan.

Idan ba a manta ba dai, Duro-Aina da kawayenta da ta gayyata wato su Oluwatoyin Faleke da Eniola Bello da Abiola Akindele, wadanda duk dalibai ne na Makarantar Sakandare ta Doregos Private Academy da ke Lagos, a Najeriya, a 2013 su ka kirkiro wannan fasahar, wadda ta zama daya daga cikin fasahohi 10 mafiya inganci a duniya, wajen rashin gurbata muhalli, da ake kira “Green invention” ko “renewable energy” a duniyar kimiyya, to amma yawancin ‘yan Najeriya ba su ma san da hakan ba, saboda rashin daukaka al’amarin.