Samar Da Gidaje Domin Masu Karamin Karfi a Kano

Sanusi Lamido Sanusi.

A wata hira da wakilin sahin Hausa na muryar Amurka Abubakar Jinaidu yayi da mai martaba sarkin Kano, Alhaji Sanusi Lamido na biyu, yayi bayani akan wani sabon tsari na hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jahar kano da sauran masarautu.

Wannan shiri dai an kirkiro shine domin gina wasu gidaje da zasu amfani matasa da kuma kananan ma’aikata a jahar Kano. Ya kuma kara da cewar dama gwamnatin jahar ta riga ta fara wannan shirin a garuruwa kamar su kwankwasiya, bandirayo da sauransu, Kuma take sayar wa manyan ma’aikata cikin sauki.

A cewar sarkin, “ wannan shirin hadin giwa na gwamnati da sauran masarautu domin ciyar da jahar kano gaba da kuma tallafawa matasa da kananan ma’aikata wata gagarumar hanya ce ta ciyar da jahar gaba da kuma tallafi ga jama’ar jahar”.

Daga karshe mai martabar yayi nuni da cewar hakan zai kara taimakawa gwamnatin ta jahar kano wajan kaddamar da shurye shirye misali kamar abinda ake kira ta turanci (social housing) wato shirin samar da gidaje a kananan hukumomi domin masu karamin karfi.

##caption:Sanusi Lamido Sanusi.##