Wani Malamin Makaranta ya Sakawa Dalibarsa Cutar Kanjamau

Dalibai Mata

Wani Malami a jihar Adamawa, dubunsa ta cika, domin an kamashi, da lalata da daya daga cikin daliban da yake koyarwa a Tafari Ganye Islamic Community Center.

Hakan ya tabbata ne bayan da aka samu daya daga cikin dalibansa na dauke da kwarar cuta mai karya garkuwar jiki, lamarin da ya kai iyayenta tsanantawa, wanda daga karshe aka gano cewa ta lalata da Malamin ne ta kamu da cutar.

A yanzu haka dai Malamin da ake tuhuma, yana hanu ‘yan sanda, inda ake cigaba da binciken ganin ko akwai wasu dalibai da wannan lamari ya shafa.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar ta Adamawa DSP. Usman Abubakar, ya tabbatar wa wakilin muryar Amurka, Ibrahim Abdulazeez,da afkuwar lamarin, ya kuma bukaci daliban, cewa idan akwai wanda irin haka ya faru dasu toh su fito, su bayyana wa hukuma, domin kin yin Magana ba zai tamaka ba.