Ya Rayu da Shan Ruwan Sama Kawai

Mahukunta a birnin New York, sun bata labarin wani mutun mai suna Donald Farrell, dan shekaru Saba’in da haihuwa cewa ya rayu ta shan ruwan sama dake sauka kan ganye har tsawon mako daya a daji baya da ya fadi a lokacin da yake farauta.

Shi dai wannan dan shekaru saba’in, ya fadi ne a lokacin da yake bin wasu dabbobi a dajin sai yayi tuntube a Avon, kusa da Buffalo.

Da yakewa ‘yan Sanda bayani Mr. Farrell, yace da ya fadi nan ya kwanta har tsawon kwanaki bakwai kafin ya samu dauki, bayan da dan uwansa ya sanarda hukumomin ‘yan Sanda cewa da uwansa bai dawo ba daga farauta.

Yanzu haka dai Mr. Farrell, na samu kulawa a asibitin Rochester a New York, inda jami’an asibitin suka ce yana cikin yanayi mai kyau.