Zanga Zangar Makiya Baki A Afirka Ta Kudu

Zimbabweans rally against recent anti-immigrant violence in South Africa, outside the South African embassy in Harare, April 17, 2015.

A kasar Afirka ta Kudu ‘yan zanga zanga sun afkawa shaguna mallakar baki ranar Asabar, a wata unguwa a birnin Johannesburg biyo bayan wata ‘barna irin wannan a wasu ‘bangarorin kasar, da suka haddasa rayukan mutane shida kamar yadda aka fitar a wani rahoto.

An zuba ‘yan sanda masu ‘din bin yawa a garin Alexandra, bayan da masu zanga zangar suka afkawa wasu shaguna, da kone tayoyin mota harma da dasa shingaye akan tituna cikin dare. Wani rahoto na cewa ‘yan sanda sun harba bindigogi masu harsashin roba, a kokarin da suke na yunkurin dakatar da tashin hankalin.

Masu zanga zangar sun lalata shaguna da motoci mallakar bakin haure a cibiyar birnin Johannesburg a ‘yan kwanakin nan.

Hare hare da ake kaiwa bakin haure wanda mafi yawancin su sun fito ne daga wasu kasashen Afirka, a ciki da ‘bangarorin birnin Durban hankali ya fara kwantawa bayan mutuwar mutane shida inji ‘yan sanda. An kame mutane 112 a lokacin tashin hankalin a yankin KwaZulu-Natal, wanda ya hada da birnin Durban.