Zauren Matasa – Rawar Da Matasa Zasu Iya Takawa A Harkar Siyasa

file photo

A cikin wannan zaman tattaunawar, Murtala Faruk da wasu matasa sun tattauna kan rawar da matasa mata da maza zasu iya takawa a cikin siyasar Najeriya.

Domin samar da cigaba a Najeriya, wata daga cikin matasan tayi kirane ga ‘yan siyasar dake kan mulki, dama wanda ke neman kujeru, da su tabbatar da sun kula da talakawan da suka zabe su domin cigaban kasa da mutanen kasar.

An bar mata a baya cikin duk wata harka ta cigaba, inji wata matashiya da cewa idan aka duba harkar gwamnati da siyasa nan ma tabbas an bar matan a baya, badan komai ba sai domin ana ganin mace bazata iya kula da wadannan harkoki na rayuwa ba. Amma a ganin matashiyar ba’a baiwa matan damar shiga da nuna rawar su kan irin wadannan harkoki na siyasa, domin a tabbatar da irin rawar da zasu iya taimakawa.

A kan maganar rashin baiwa mata dama domin a taka dasu a fagen siyasar Najeriya, wani matashi na ganin cewa maza sun mamaye ko ina a fagen siyasa, harma yana ganin idan aka baiwa mata damar shiga siyasa zasuyi iya bakin kokarin su wajen bada gudunmawar su ga dimokaradiyya, amma yayi kira ga cewa sai ana saka su a hanya kasancewar mata nada rauni.

Dan gane da faruwar rikice rikice, musammam a tsakanin matasa dangane da bin ‘yan siyasa, rashin ilmi shine ginshiki hakan kasancewar ana amfani da matasa wajen basu kudi da kayen maye domin biyan bukatun ‘yan siyasar.

Daga karshe wani matashi yayi kira ga mutane da su fita su jefa kuri’ar su ranar zabe, sannan su bar gurin, kuma a guji karbar kudade daga hannun ‘yan siyasa.