Ziyarar Kungiyar Samarin Musulmi Dana Krista Zuwa Jihar Bauchi.

Matasa sun taru suna wakoki

Kungiyar samarin musulmi dana krista mai suna ACAC a taikaice, mai da’awar ganin ta farfado da irin zamantakewar dake wanzuwa a tsakanin mabiya addinan biyu, tun zamanin kaka da kakanni ta kawo ziyara jihar Bauchi.

Kungiyar dai ta ziyarci shugabannin addinan biyu domin fahimtar dasu irin abubuwan da kungiyar ke kokarin cimmawa. Barista Sadiq Ilela, shine shugaban kungiyar na kasa, inda yace, “wannan kungiyace wadda ta hada matasa na arewacin Najeriya, don cigaban wannan yanki na arewa, kuma daga cikin dalilin da mukayi nazari da shi wajen kafa wannan kungiyar shine maganin matsaloli irin wadanda ke damun mu, na rashin zaman lafiya da rashin fahimta, da kuma rashin darajantawa da mutunta addinan juna dakuma matsayin juna akan rayuwa gaba daya.”

Shi kuma shugaban kungiyar krista na shiyyar maso gabas Raveran dakta Sha’aibu Bell, ya bayyana manufar kungiyar da cewa abin yabawa ne, kuma ya tabbatar da amfanin matasa ga wannan dimokaradiyya tamu da yanzu kasancewar matasan sune shugabannin gaba, da jan kunne kan kada kowa ya bari a yaudareshi musammam ma a wannan lokaci na guguwar siyasa a kasa.

A jawabin kwamishinan hukumar shara’ar musulunci Mustapha Baba Ilela, yace kungiyar zata taimaka wajen shawo matsalar matasa a kasa baki daya, yakuma yi alkawarin bada shawarwari na tsakani da Allah, ha’ila yau yayi fatan alkhairi ga wannan kungiya ta ACAC, ya kuma rufe da cewar matasa sune ginshikin kowacce al’umma, kuma sune kashin bayan ko wacce al’umma, idan matasa suka lalace to al’umma ta shiga uku.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Musulmai da Krista - 3'28"