Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ba Kanfanin Volkswagen Wa'adin Kwana Bakwai


Hukumar kare hakkin masu anfani da kayayyaki da masa'antu suka sarraf ta Najeriya ta ce ta lura kamfanin Volkswagen ya amince cewar ya sanya wata na'ura a motar wadda zata hana gane ainihin irin hayakin da motar take fiddawa.

Motocin dai sun kunshi kirar Golf, da Jetta, da Billtle da kuma Passat. Hukumar ta umurci kanfanin Volkswagen da yayi bayanin motoci nawa ne abin ya shafa a Najeriya, kuma wanne mataki take bi domin janye wadannan motoci daga cikin kasar.

Mr Abiodun shine daraktan hulda da jama'a na hukumar kare hakkin masu anfani da kayayyaki kuma ya yiwa wakilin sashin Hausa Hassan Maina Kaina daga birnin Abuja karin bayani inda ya ce;

"Alhakin hukumar ne ta kare hakkin jama'a masu anfani da kayayyakin da masana'antu suka sarrafa a Najeriya, dan haka wannan batu ne na tattalin arzki domin masu anfani da motocin da kuma lafiyar su. Saboda haka duk abinda ka sa kudin ka ka saya, dole kwalliya ta biya kudin sabulu."

A mayar da martanin tambayar da wakilin ya yi masa cewar idan kamfanin ya yi kunnen uwar shegu da maganar fa, sai ya budu baki ya ce.

"idan aka tuhume ka bisa ka'ida kuma ka yi kunnen uwar shegu da batun to lallai shima laifi ne."

Dr Isma'il Ammani wani kwararren masanin muhalli ne a birnin London amma ya kai ziyara Abuja inda ya yi bayanin cewa a kwai matsaloli da dama dangane da irin wannan hayaki da motar ke fitar wa wadanda suka hada da ciwon zuciyza da sauran su.

Ga cikakken rahoton.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG