WASHINGTON, DC —
A shirinmu na nishadi a yau dandali ya samu zantawa da wani mawaki Sa'ad Mustapha Suleman wanda aka fi sani da SD Nagudu ya fara waka a shekara ta 2010.
Ya ce ya tsinci kansa cikin harkar waka ne sakamakon yadda ya ga abokansa na harkar waka da kuma sha'awar da ya keyi na waka domin ya dade da sha’awar abun a ransa .
Yana mai cewa yin waka wani fagge ne na aikawa da sako ga jama’a, kuma ganin cewa yana da sakoni da ya keso ya mika ga jama’a yasa ya dage ya soma yaka domin cika burinsa.
Malam, Sa’ad Suleman, ya ce a duk lokacin da yake waka yana samun anashiwa domin yin waka wani buri ne da yake dashi da dadewa amma yanzu burin ya cika.