Ministan matasa da wasani na Najeriya Barrister Solomon Dalung, yace cin hanci da rashawa da dabi’un tsubbuce tsubbuce shine ya yiwa ci gaban wasani a Najeriya, katutu, kuma ya sha alwashin cewa sai yaga bayan hakan.
Ministan wanda ya furta hakan a Ingila, yace ya dukufa ganin cewa yayi wajen da duk masu dabiyar cin hanci da maido da gudane gudanen hukumar a bayane abinda zai maido da martaban wasani a Najeriya.
Ya kara da cewa tsubbuce tsubbucen ya kai ga cewa a wasu lokuta ‘yan wasa sai sun amince da bada kudi gabin ko kuma wani bangare na kudadensu kafin a zabe su su yiwa kasar wasa, abinda yace zai yi magani afkuwar haka nan gaba.
Ya kuma danganta tabarbarewar filayen wasani da mummunar cin hanci da wannan bangaren ya dade yana fama dashi.
Ministan na mai cewa bayan wasani Olympics za’a yiwa hukumar wasani ta Najeriya garanbawul wanda zai kasance sai wadanda zasu tabuka abin arzikin ne zasu kasance a hukumar.
w