Sarki Sanusi yace suna cike da juyayi game da gobarar da ta faru a kasuwar Sabongarin Kano da ake kira Kasuwar Muhammad Rimi.
Yace ba da dadewa ba aka yi rin gobarar a kasuwar Kurmi da kasuwar Kwanar Singa. Kasancewa Kano cibiyar ciniki da kasuwanci ce a Najeriya gaba daya har ma da wasu kasashen Afirka irin wannan gobarar istilai ce ga kasuwanci da tattalin arziki.
Sarki Sanusi yace suna jajantawa duk wadanda gobarar ta shafa da al'ummar Kano da gwamnatin jiha. Yayi addu'a Allah ya maida alheri, ya kuma kiyaye gaba tare da maido da sabon arziki.
Bayan da ya gama yi masu jaje Sarkin yace wajibi ne ya jawo hankalin jama'a cewa duk lokacin da irin wannan bala'in ya faru to bayan addu'a dole ne mutane su binciki kansu. Jama'a su duba tsakaninsu da Ubangiji domin gujewa fushinsa. Yace lallai su dubi tsakaninsu da sauran bayin Allah domin gujewa yin zalunci.
Sarkin ya cigaba da cewa su dinga yiwa juna nasiha a duka lamuransu. Ya kirasu su mayar da hankali akan yawan sadaka da kula da marayu da mata da yara da raunatattu. Ya gargadesu su dinga fitar da zakka a cikin dukiya.
Da ya juya kan gwamnatoci da kamfanoni da jama'a sai ya kira a hada kai domin tallafawa wadanda bala'in ya shafa.
Dangane da yadda aka gina kasuwannin Kano yace lokaci ya yi da za'a sake duba fasalinsu akan yadda ake ciniki da ajiye kaya cikinsu. Yadda zamani ke canzawa yakama su yi tafiyar da ta dace da zamanin muddin ba'a sabawa shari'a ko kyawawan al'adunsu ba.Yace hakan zai kawo masu cigaba mai albarka.
Ya kira al'umma da su yi kokari suna ajiye kudi a bankuna ba a shaguna ba. Ya kira a rungumi tsarin insura da aka ginashi akan tsarin shari'a saboda mayarda dukiya idan irin wannan bala'i ya auku.
Sarki Sanusi ya kira hukumar jiha da ta tarayya su gudanar da bincike akan abun dake haddasa irin wannan gobarar a kasuwoyi da makarantu. Yana fata za'a duba fasalin kasuwoyin gaba daya a bude hanyoyin da aka toshe saboda gaggawar agaji. Jama'a kuma su yi hakuri akan gyare-gyaren da suka zama dole domin a kare rayuka da dukiyar jama'a.
Ya kira jama'a da su gaggauta komawa harkokin ciniki da bunkasa tattalin arziki. Su yi kokari wajen bunkasa harkokin noma da masana'antu.
Ga karin bayani